in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe asibitocin bogi sama da 100 a Najeriya
2018-11-15 09:41:42 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mahukuntan kasar sun sanar da rufe asibitoci 108 a jihar Nasarawa dake yankin arewa maso tsakiyar kasar.

Darektan kula da asibitoci na jihar Nasarawa Haruna Ekom ya shaidawa manema labarai a garin Lafia, babban birnin jihar cewa, an rufe wadannan asibitoci ne saboda rashin takardun izni daga gwamnati, da rashin sabunta lasisinsu. Ya ce, an dauki wannan mataki ne bisa ga irin bayanan da gwamnati ta tattara a wurare daban-daban da abubuwan da tawagar masu bincike daga ma'aikatar lafiyar jihar suka gani yayin ziyarar gani da ido.

Ya ce, ma'aikatar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tsaftace sashen lafiyar jihar, ta hanyar tabbatar da ganin asibitocin jihar na gudanar da ayyukansu bisa ka'idojin kasa da kasa.

Ekom ya kuma gargadi masu asibitocin da ba su da lasisi da ma jami'an lafiyar da ba su cikakkiyar kwarewar aiki, da su guji yin haka ko kuma doka ta yi aiki a kansu.

Likitocin bogi dai sun yi kaurin suna wajen duba marasa lafiya a Najeriya, da nufin samun kudi. Koda a watan Oktoban shekarar 2017 ma, sai da kungiyar likitocin kasar ta fito karara tana kira ga majalisar dattawan kasar, da ta sanya hannu kan dokar nan dake yaki da likitocin bogi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China