in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yayin da take fuskantar karanci jini, Sudan ta Kudu ta yi kira da a taimaka mata
2018-06-15 11:17:02 cri
Sudan ta Kudu ta yi bikin ranar bada gudunmuwar jini ta duniya a jiya Alhamis, inda ta yi kira da a taimakawa harkokin bada jini a fadin kasar da rikici ya daidaita a gabashin Afrika.

Ministan lafiya na kasar Reik Gai Kok, ya ce 'yar autar kasar a duniya, ba ta da ingantattun cibiyoyi da kayakin kiwon lafiya da za ta yi amfani da su wajen gudanar da shirin bada jini, amma dai, ana kokarin inganta yanayin.

Reik kok, ya ce duk da babu wata kiddidiga a hukumance game da adadin mace-macen da karancin jini ya haifar, mutane da dama na ci gaba da mutuwa saboda rashin ayyukan bada jini, tunda cibiyar badawa da adana jini daya tak kasar ke da ita.

A cewar Evans Liyosi, wakilin hukumar lafiya ta duniya WHO a Sudan ta Kudu, rashin ayyukan bada jini a fadin kasar da rikici ya daidaita, na barazana ga lafiyar al'umma.

Evans Liyosi, ya yi kira da hukumomin bada taimako na duniya, su taimakawa Sudan ta Kudu fadada cibiyarta na bada jini domin rage yawan mutuwar mutane saboda karancin jini, musammam a tsakanin yara da mata masu juna biyu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China