in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mace-macen mata yayin haihuwa ya zarce na cutukan malaria da tarin fuka a yammacin Afrika
2018-06-06 10:16:34 cri

Rahoto na shekarar 2017, da hukumar kiwon lafiya ta yankin yammacin Afrika (WAHO), ta wallafa jiya a Banjul, ya nuna cewa, adadin mace-mace mata yayin haihuwa a yankin, ya zarce wadanda cutukan da ake samu a yankuna masu zafi, ciki har da cutar malaria da tarin fuka ke haifarwa.

Da yake gabatar da rahoton, Daraktan sashen tsare-tsare da bincike da bayanan lafiya na hukumar Salifou Zouma, ya shaidawa wakilan yankin cewa, kasashe 14 na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS, ban da kasar Cape Verde, sun bada rahoton mutuwar mata yayin haihuwa guda 5,084 a cibiyoyin kiwon lafiya.

Ya ce duk da kiyasin da aka yi, ya yi kasa saboda rashin isassun bayanai, adadin ya fi na jimilar mutuwar da cutukan da aka fi samu a yankin suka haifar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China