Wu Haitao wanda ya bayyana haka a taron kwamitin sulhu, ya ce, shekarun da aka kwashe ana tashin hankali a kasar ta Syria, ya haifar wa kasar da ma al'ummar ta mummunan kunci. Don haka al'ummar Syria na bukatar samun zaman lafiya cikin hanzari ta yadda za su koma, su kuma farfado da rayuwarsu kamar yadda aka saba.
Ya ce, ya kamata MDD ta zurfafa tsare-tsaren da take yi da gwamnatin Syria, ta yadda za a hanzarta kafa kwamitin da zai shata kundin tsarin kasar wadda zai kunshi kowa ya kuma samu amincewar dukkan bangarori.
Jami'in na kasar Sin ya kuma bayyana cewa, wajibi ne a yi la'akari da bukatun bangarorin da abin da ya shafa yadda ya kamata, ciki har da gwamnatin Syria, ta yadda za a kafa tsarin siyasa mai nagarta da zai dore.
Ya bukaci al'ummomin kasa da kasa, da su karfafa hadin gwiwar yaki da ayyukan ta'addanci a kasar Syria, da amfani da ingantaccen tsari don yakar dukkan kungiyoyin 'yan ta'adda da kwamitin sulhu ya zayyana, don ganin ba su sake dawowa ba.(Ibrahim)