Jakadan kasar Sin a Syria Qi Qianjin, ya bayyana muhimmancin cigaba da hadin gwiwa tsakanin Sin da Syrian a bangaren watsa labarai.
Da yake jawabi a hedkwatar jaridar al-Watan ta kasar a Damascus, Qi ya yaba da irin hadin gwiwar dake wanzuwa tsakanin kasashen biyu a cikin shekaru 7 da suka gabata a matakai daban daban, ciki har da hadin gwiwar kasashen a bangaren yada labaru.
Jakadan ya ce, "muna sha'awar wannan hadin gwiwa, kuma muna son mu ci gaba da hadin gwiwar a wannan bangare. Muna yin tunani game da sabbin ayyukan yin musaya tsakanin 'yan jaridun Sin da na Syria a nan gaba".
A nasa bangaren, Waddah Abd Rabbo, babban editan jaridar ta al-Watan ya ce, kafafen yada labaran Syrian suna bukatar a ci gaba da taimaka musu sakamakon kalubalolin da suke fuskanta a sanadiyyar tashin hankalin da kasar take fama da shi.
"Muna son cigaba da yin hadin gwiwa da Sin" in ji Abd Rabbo.(Ahmad Fagam)