in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana sa ran ci gaban shawarwarin sulhu kan batun Syria
2017-06-18 13:01:29 cri
A jiya Asabar, manzon musamman na gwamnatin kasar Sin Xie Xiaoyan, wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar Syria ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana yin shawarwari da bangarorin da batun rikicin kasar Syria ya shafa, domin ciyar da shawarwarin neman sulhu kan batun Syria gaba, ta yadda bangarorin da abin ya shafa za su iya warware matsalar kasar Syria ta hanyar siyasa.

A yayin taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Xie Xiaoyan ya ce, kasar Sin tana sa ran za a kulla wasu yarjejeniyoyi a yayin taron shawarwarin neman sulhu, da aiwatar da su yadda ya kamata, ta yadda za a samu fahimta a tsakanin kabilu daban daban na kasar Syria, sa'an nan, za a iya samun fahimtar juna a tsakanin kabilu da gwamnatin kasar ta Syria.

A sa'i guda kuma, kasar Sin ta dukufa wajen ba da taimakon jin kai ga al'ummomin kasar, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta samar da taimakon jin kai da darajar su ta kai dallar Amurka miliyan 680 ga kasar Syria da wasu kasashen dake yankin.

Bugu da kari, Mr. Xie ya jaddada cewa, 'yan ta'adda su ne abokan gaba na dukkanin bil Adama a nan duniya, ya kamata bangarori daban daban na kasar Syria, da kasashen dake yankin da kuma gamayyar kasa da kasa su yi hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci, bai kamata a nuna bambanci a yayin gudanar da ayyukan yaki da ta'addanci ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China