in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin ya bukaci a kara daukar matakan dakile sake kafuwar kungiyoyin 'yan ta'adda a Syria
2019-03-01 11:26:05 cri

Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya fada a ranar Alhamis cewa, kamata ya yi al'ummar kasa da kasa su kara azama tare da yin hadin gwiwa don yakar ayyukan ta'addanci, da samar da cikakken tsarin zaman lafiya, kana da kawar da dukkan kungiyoyin ta'addanci wadanda kwamitin sulhun MDD ya lissafa su, kana a tabbatar da daukar matakai na hana sake kafuwar kungiyoyin 'yan ta'adda domin dakile aniyarsu na kawo barazana ga yanayin zaman lafiya da tsaro.

A lokacin taron kwamitin sulhun MDD game da halin siyasar da ake ciki a kasar Syria, Wu ya yi gargadin cewa, "akwai yiwuwar kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Idlib za su sake tsayawa da kafafunsu, wanda hakan babbar barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar Syria kuma hakan zai iya yin kafar ungulu ga shirin sake gina kasar da komawar 'yan gudun hijira zuwa kasar ta Syria."

Kasar Sin tana maraba da taron da shugabannin kasashen Rasha, Turkiyya da Iran suka shirya a birnin Sochi a ranar 14 ga watan Fabrairu, domin tattaunawa game da halin da ake ciki a Syria kuma sun fitar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka jaddada aniyarsu ta kakkabe kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar wanda kwamitin sulhun MDD ya zayyana da kuma aniyar da kasashen ke da ita na tabbatar da warware rikicin kasar ta Syria ta hanyar siyasa, in ji wakilin na kasar Sin.

Ya kamata al'ummar kasa da kasa su mayar da hankali wajen ci gaba da daukar matakan da za su wanzar da zaman lafiya da warware rikicin kasar Syria ta hanyar siyasa," in ji Wu.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China