in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: yaki da ta'addanci, yin tattaunawa, sake gina kasa, muhimman fannoni 3 da za a mai da hankali a kai yayin da ake daidaita batun Sham
2017-11-24 19:59:01 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da mai ba da shawara ga shugaban kasar Sham ta fuskar siyasa da labarai madam Bouthaina Shaaban, a yau Jumma'a 24 ga wata a nan Beijing.

Yayin ganawar tasu, Wang Yi ya ce yanzu haka an shiga wani sabon mataki na daidaita batun Sham a siyasance. Ya ce yaki da ta'addanci, da tattaunawa, da sake gina kasa, su ne muhimman fannoni 3 da za a mai da hankali a kai yayin da ake daidaita batun kasar Sham.

Mr. Wang Yi ya ce kamata ya yi a tattauna tsakanin sassa daban daban bisa tushen yaki da 'yan ta'adda, da tabbatar da an farfado da kasar ta Sham. Kaza lika kasar Sin na fatan cewa, Sham za ta amfani damarta, ta nuna ra'ayin sassauci, a kokarin samun sakamakon a-zo-a-gani yayin tattaunawar.

A nata bangaren, madam Shaaban ta amince da ra'ayin mista Wang Yi, dangane da batun Sham. Ta kuma yaba wa ra'ayin kasar Sin na adalci. Ta yi nuni da cewa, gwamnatin Sham na fatan shiga aikin warware batun kasar a siyasance, tana kuma maraba da gudummawar kasar Sin a wannan fanni. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China