in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da yunkurin ganin an warware rikicin Syria a siyasance
2017-09-22 10:10:12 cri

Wakilin musammam na kasar Sin game da rikicin kasar Syria, Xie Xiaoyan, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da tuntubar bangarorin dake da alaka da rikicin Syria da aiki don ganin an hau teburin sulhu tare kuma da ba da gudummuwa wajen ganin an warware rikicin a siyasance.

Xie Xiaoyan wanda ke ziyara a Moscow, ya bayyana haka ne a jiya, inda ya ce kasar Sin za ta ci gaba da samar da agaji ga 'yan gudun hijirar Syria dake ciki da wajen Syria.

Yayin ziyarar, jami'in ya gana da mataimakin Ministan harkokin wajen Rasha Mikhail Bogdanov, inda suka tattauna game da matsalolin Gabas ta Tsakiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China