Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya furta a yau Laraba cewa, kasar Sin tana tsayawa kan manufarta ta nuna gaskiya, da sahihanci, da kulla hulda mai kyau, gami da samar da takamaiman sakamako, da kuma ra'ayin kasar na nuna adalci a kan moriyar juna, yayin da take hadin gwiwa da kasashen Afirka, manufofin da suka samu karbuwa tsakanin al'ummomin nahiyar Afirka, gami da amincewar gamayyar kasa da kasa.
Kafin haka, Jean Juncker, shugaban majalisar kungiyar tarayyar Turai, ya bayyana a kwanakin baya cewa, tallafin da kasar Sin ta baiwa Afirka ya sanya kasashen dake nahiyar Afirka da yawa shiga matsalar bashi fiye da kima. Dangane da wadannan kalamai, Madam Hua ta ce, babu wata kasa dake nahiyar Afirka wadda ke fama da matsalar bashi sakamakon hadin gwiwa da kasar Sin. A cewar jami'ar kasar Sin, tsarin tattalin arziki maras adalci da ake amfani da shi yanzu a duniyarmu,na daga cikin manyan dalilan da suka sababa matsalar bashi fiye da kima da wasu kasashen nahiyar ke fama da ita. (Bello Wang)