A jawabinsa yayin bikin kaddamar da rahoton, jakadan kasar Sin a Afirka ta kudu Lin Songtian ya bayyana cewa, 'yan kasuwar kasar sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki da jin dadin rayuwar al'ummar kasar Afirka ta kudu, suna kuma martaba dokokin kasar yadda ya kamata.
Jakada Lin ya ce, 'yan kasuwar kasar Sin dake Afirka ta kudun sun kuma kulla zumunta mai karfi da mazauna wurin, da samar musu da ababan more rayuwa, kamar bangaren Ilimi da kayayyakin kiwon lafiya da sauransu.
Rahoton ya ce, kamfanonin kasar Sin za su ci gaba da zuba jari, da gudanar da harkokinsu bisa doka, tare da kara daukar ma'aikatan wurin.(Ibrahim)