Sin na fatan kasashen duniya za su kalli dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka da idon basira
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau Litinin cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" shawara ce da Sin ta gabatar domin kula hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasashen duniya, ba ta da nasaba da batun harkokin siyasa, kuma ba domin yin gasa da wani ko wata ba. Muna fatan sauran kasashen duniya za su kalli hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa da idon basira.
Ta ce, ya kamata su taimakawa kasashe masu tasowa kamar yadda kasar Sin take yi a halin yanzu, a maimakon furta kalaman da ba su dace ba.
Rahotanni na cewa, a kwanan baya, mataimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa John Robert Bolton ya bayyana cewa, Sin da Rasha suna son kara tasirinsu a nahiyar Afirka a fannin sha'anin hada hadar kudi da na siyasa, domin yin gasa da kasar Amurka. (Maryam)