in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira da a taimakawa kasashen dake kahon Afirka
2018-11-15 10:28:04 cri

Wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu ya yi kira ga kwamitin sulhun MDD da al'ummomin kasa da kasa da su samarwa kasashen da ke yankin kahon Afirka taimakon da ya dace

Ma Zhaoxu wanda ya bayyana hakan yayin taron kwamitin sulhun majalisar game da kasar Somaliya, ya ce, alaka tsakanin kasashen yankin na ci gaba da inganta a 'yan shekarun baya-bayan nan.

Jami'in ya ce Kasar Sin tana fatan kasashen dake yankin za su yi kyakkyawar amfani da wannan dama wajen karfafa tattaunawa da tuntubar juna, su kuma yi kokarin warware bambance-bambancen dake tsakaninsu.

Yayin wannan zama, kwamitin sulhun ya amince da kudurin bai daya na dage takunkumin hana sayar da makamai na kusan shekaru goma da ma wasu takunkumai da aka kakabawa kasar Eritrea, biyo bayan mataki na baya-bayan da kasar ta dauka na sasantawa da makwabtanta dake yankin.

Jami'in na Sin ya kuma bayyana cewa, dage takunkumin zai taimakawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban yankin.

Ya kuma yi alkawarin cewa, kasarsa za ta ci gaba da hada kai da ragowar kasashen duniya, wajen taka rawar da ta dace a kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ci gaba a kasashen dake yankin kahon Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China