in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da shugaban jami'ar Harvard ta Amurka
2019-03-20 19:41:32 cri

Yau Laraba ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da shugaban jami'ar Harvard ta kasar Amurka Lawrence Bacow a nan Beijing.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya ce, kasar Sin na tsayawa kan yin koyi da juna, tana kuma karfafa gwiwar yin karatu a ketare, tare da goyon bayan yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen waje ta fuskar ba da ilmi. Ya yi fatan cewa, Sin da Amurka za su kara samun sakamako ta fuskar mu'amalar al'adu. Shugaban kasar Sin ya jaddada cewa, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga waje ta fuskar ba da ilmi, inganta yin mu'amala da koyi da juna da kasashen duniya, a kokarin kara inganta harkar ba da ilmi. Don haka kasar Sin tana son kara yin mu'amala da hadin gwiwa da hukumomin ba da ilmi da nazarin kimiyya na Amurka ciki had da jami'ar Harvard.

A nasa bangaren, mista Bacow ya ce, ya yaba da yadda gwamnatin Sin take ba ba muhimmanci da kuma kara karfin ba da ilmi mai zurfi. Jami'arsa na son ci gaba da yin mu'amala da hadin gwiwa da hukumomin ba da ilmi da nazarin kimiyya na kasar Sin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China