in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Xi a Turai za ta bunkasa kawancen Sin da EU, in ji Wang Yi
2019-03-19 09:34:04 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce ziyarar da shugaba Xi Jinping zai gudanar a Italy, da Monaco da Faransa, za ta samar da damar bunkasa kawancen Sin da kungiyar tarayyar Turai ta EU daga dukkanin fannoni.

Wang Yi ya bayyana hakan ne, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tsakanin sa da wakiliyar musamman ta kungiyar EU a fannin harkokin waje da tsaro Federica Mogherini. Jami'an biyu sun zanta da 'yan jaridu a jiya Litinin a birnin Brussels.

Cikin tsokacin sa, Mr. Wang Yi ya ce shugaba Xi Jinping zai gudanar da ziyarar sa ne tsakanin ranekun 21 zuwa 26 ga watan nan na Maris. Ya ce shugaba Xi ya zabi ziyartar Turai a farkon wannan shekara ne, duba da muhimmancin da yake dorawa ga dangantakar sassan biyu.

Mr. Wang ya kara da cewa, ziyarar na nuna cewa, duk da yanayin da ake ciki a mataki na kasa da kasa, Sin za ta ci gaba da daukar Turai a matsayin muhimmiyar kawa ta hadin gwiwa, za kuma ta ci gaba da daukar nahiyar a matsayin abokiyar hulda mai daraja a fannonin ta na diflomasiyya.

Wang ya kara da cewa, wannan ziyara za ta samar da karin daidaito, da bunkasa alakar sassa daban daban a duniyar yau, kana hakan zai kuma tallafa wajen hade sassan nahiyar Turai da Asiya, zai kuma fadada ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China