in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai fara ziyararsa ta farko a shekarar 2019 a kasar Italiya
2019-03-20 19:38:29 cri

Ranar 21 ga watan Maris, shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai fara ziyararsa ta farko a shekarar bana, inda zai ziyarci kasashe 3 na Turai, kuma kasar Italiya ita ce zango na farko.

Bana, shekaru 15 ke nan da kulla huldar abokantaka a tsakanin Sin da Italiya daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare. Kuma shekara mai zuwa, shekaru 50 da kulla huldar jakadanci a tsakanin kasashen 2. A daidai wannan lokaci, ziyarar da shugaban kasar Sin zai kai Italiya tana da ma'ana sosai wajen raya huldar da ke tsakanin kasashen 2.

Shirin Sin da Italiya na inganta hadin gwiwarsu kan shawarar "ziri daya da hanya daya" ya jawo hankali a ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai Italiya. Kasashen 2 sun nemi kafa "ziri daya da hanya daya" ta sabon zamani ta sama, kasa da kuma teku, a kokarin kara kawo wa jama'arsu alheri. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China