in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A saurari hirar da shugaba Xi Jinping ya yi da wakilan jama'a
2019-03-13 15:35:16 cri

A duk lokacin da yake rangadi a sassan kasar Sin, ko kuma yake shawarwari da wakilan jama'a yayin taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (CPC) da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar(CPPCC), kullum shugaban kasar Sin Xi Jinping na mai da hankali sosai kan sauraron ra'ayoyi daga al'umma. A yayin taruka biyu na wannan shekara, wakilan makiyaya da na manoma da ma na masana'antu da kuma wakilan da suka fito daga yankunan da ke fama da talauci sun gana da shugaban, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi bunkasa kasa ba tare da gurtaba muhalli ba, da farfado da yankunan karkara da kirkire-kirkire da saukaka fatara da dai makamantansu.

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada bukatar kara himma wajen bullo da dabarun da za su taimaka wajen gina muhallin halittu da zai dace da zamani, da kare wurare masu kayatarwa dake kan iyakar arewacin kasar.

Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar JKS, kana shugaban kwamitin koli na rundunar sojojin kasar, ya bayyana hakan ne lokacin da ya halarci zaman tattaunawa da wakilan yankin Mongoliya ta gida yayin zaman taro na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar na 13 dake gudana yanzu haka a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China