in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya aike da sakon jaje zuwa ga New Zealand
2019-03-16 15:55:17 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon jaje ga gwamna janar na New Zealand Patsy Reddy, bisa mummunan harin da aka kai birnin Christchurch na kasar a jiya Juma' a.

Cikin sakonsa, shugaba Xi ya ce, ya kadu da jin labarin harbe-harben da suka rutsa da mutane da dama.

Ya ce, a madadin gwamnati da al'ummar kasar Sin da ma shi kansa, yana jajantawa tare da mika ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar New Zealand, yana kuma mai yi wa wadanda suka raunana fatan samun sauki cikin gaggawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China