Baya ga haka, a cikin wasikar Xi Jinping ya ce, makarantarsu ta cimma nasarar kafa makarantar sakandare ta kasa da kasa ta Sinanci dake karatu a fannonin da suka shafi ilmin lissafi da sauransu, kuma ta horar da matasa masu nufin gudanar da aikin sada zumunta tsakanin Sin da Italiya masu yawa. Xi Jinping ya kuma yaba sosai da makarantar, sakamakon kokarinta na inganta musayar ra'ayoyi da cudanyar al'adu a tsakanin matasan kasashen biyu, da ciyar da zumunta a tsakanin jama'ar kasashen biyu gaba. A cewarsa, yana maraba da daliban makarantar su yi karatu da aiki a kasar Sin, yana mai fatan kasar Sin za ta kasance wurin da za su cimma burinsu. (Bilkisu)