in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron manema labaru game da ziyarar shugaba Xi Jinping a kasashen Italiya da Monaco da Faransa
2019-03-20 14:29:41 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gudanar da taron manema labaru a yau Laraba, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Wang Chao ya yi bayani game da ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai a kasashen Italiya, da Monaco, da Faransa tare da amsa tambayoyin 'yan jarida.

Wang Chao ya yi nuni da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai kai ziyara a kasashen Italiya, da Monaco, da kuma Faransa tun daga ranar 21 zuwa 26 ga wannan wata. Wannan ne ziyararsa ta farko a bana, wadda tana da babbar ma'ana ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen uku.

Wang Chao ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping da firaministan kasar Italiya Giuseppe Conte za su duba aikin sa hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa na gwamnatocin kasashen biyu a fannonin harkokin diplomasiyya, da tattalin arziki da cinikayya, da al'adu da dai sauransu, da kuma yarjejeniyoyin gina ayyukan more rayuwa, da injiniyoyi, da hada-hadar kudi da sauransu. Kana kasashen biyu za su kara yin hadin gwiwa wajen raya shawarar "ziri daya da hanya daya", don amfanawa jama'arsu gaba daya.

Game da ziyarar Xi a kasar Monaco, shugaba Xi zai yi shawarwari tare da sarkin kasar Yarima Albert II, inda za su yi mu'amala a fannonin hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu, da kiyaye muhalli da sauransu, don bude sabon babi wajen raya dangantakar dake tsakaninsu.

Game da ziyarasa a kasar Faransa, shugabannin Sin da Faransa za su yi musayar ra'ayoyi kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa da Turai, kuma manyan batutuwan duniya da yankuna, kana za su duba aikin daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwarsu a fannonin makamashi, da sufuri, da aikin gona, da hada-hadar kudi, da al'adu, da kimiyya da fasaha da sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China