David Monyae, ya yi wannan tsokaci ne a jiya, yayin da yake gabatar da jawabi game da dangantakar Sin da Afrika, a Jami'ar Witwatersand dake Johannesburg na Arika ta Kudu.
Ya ce dangantakar ta zarce wadda bangare guda kadai zai amfana, yana mai cewa dukkan bangarorin biyu sun amfana. Ya ce abu mai muhimmanci ne kulla alaka da kasar Sin, wadda ta mamaye kaso 15 na tattalin arzikin duniya da kuma kaso 37 na kasashe masu tasowa.
Ya ce kasar Sin na son kawar da talauci da samar da sabon yanayi a duniya, ta yadda babu wata kasa da za ta yi mulkin mallaka kan wasu.
Daraktan ya kuma bukaci a daina sauraron zantuttukan da ake yi game da basukan da kasar Sin ke bayarwa, domin nata bashin, bai kai na kasashen yammacin duniya ba.
Ya ce makomar Afrika ta dogara ne kan muhimmiyar dangantakarta da Kasar Sin, yana mai cewa kasar ta taimaka wajen raya kayakin more rayuwa a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)