in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe: Mummunar mahaukaciyar guguwa ta yi sanadin mutuwar mutane 31
2019-03-17 16:11:40 cri

Ranar 16 ga wata, gwamnatin kasar Zimbabwe ta bayyana cewa, mummunar mahaukaciyar guguwa ta Idai, wadda ta sauka a gabashin kasar a daren ranar 15 ga wata, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 31, yayin da wasu gomai suka yi batan-dabo.

Ma'aikatar yada labaru ta kasar Zimbabwe ta ba da labari ta shafin sada zumunta cewa, mahaukaciyar guguwar ta Idai ta kai mummunan hari a yankunan Mutare, Chipinge da Chimanimani dake lardin Manicaland a gabashin kasar. Mutanen dake zaune a yankin Chimanimani sun fi fama da bala'in.

Yanzu haka gwamnatin kasar Zimbabwe ta aika da kungiyoyin ceto zuwa wuraren da bala'in ya rutsa da su. Amma ambaliyar ruwan ta lalace wasu hanyoyin mota da kuma gadoji, shi ya sa kungiyoyin ceton sun gamu da matsala wajen shiga wuraren da bala'in ya shafa. Har ila yau, rundunar sojojin kasar Zimbabwe ita ma ta tura sojoji domin shiga aikin ceto, wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa wata makarantar dake yankin Chipinge domin ceton 'yan makarantar kusan dari 2 daga ambaliyar ruwan, inda makarantarsu ta rushe sakamakon ambaliyar ruwan.

A cikin duhun daren ranar 14 ga wata bisa agogon Zimbabwe, mahaukaciyar guguwar ta Idai ta sauka a yankunan dake dab da teku a tsakiyar lardin Sofala, kuma ta fara kai hari a gabashin kasar daga daren ranar 15 ga wata. An yi hasashen yanayi cewa, ya zuwa yanzu mahaukaciyar guguwar ta Idai tana gabashin kasar Zimbabwe. An yi hasashen cewa, za a kara yin ruwan sama kamar da bakin karya a wurin. Don haka mai yiwuwa ne yawan wadanda bala'in ya rutsa da su da kuma wadanda suka rasa rayukansu sakamakon bala'in zai karu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China