"Kofa a bude take a kokarin da muke na neman yadda za mu samarwa kasarmu kyakkyawar makoma, da ci gaba, da ingantacciyar rayuwa ga al'ummarmu," Mnangagwa ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi wanda aka karanta a madadinsa a taron addu'o'i na kasa na mabiya addinin kirista.
A ranar Laraba Mnangagwa, ya gana da 'yan takarar neman shugabancin kasar su 20 wadanda suka tsaya takarar a zaben da aka gudanar a bara domin tattaunawar bayan zabe da nufin lalibo bakin zaren warware manyan kalubalolin dake addabar kasar. (Ahmad Fagam)