in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya soke ziyarar Davos don tinkarar wutar data kunno kai a kasar
2019-01-21 10:42:08 cri
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya soke ziyararsa zuwa birnin Davos, na kasar Switzerland, inda zai mayar da hankali game da batun matsalar data kunno kai a kasarsa.

A sakonsa na Twitter, Mnangagwa yace ya yanke ziyarar ne nan take don halartar wasu muhimman batutuwa da suka shafi harkokin cikin gidan kasarsa.

"A bisa yanayin da ya shafi tattalin arziki, zan koma gida bayan halartar babban taron kasashe kan batun ciniki da zuba jari," ya bayyana hakan ne a da yammacin ranar Lahadi.

"Ministan kudi Mthuli Ncube shine zai wakilcemu a taron na Davos. Abu na farko dana bada fifiko shine na kwantar da hankalin al'ummar kasar Zimbabwe, a samu kwanciyar hankali da kuma cigaba da ayyuka," inji shi.

A makon jiya al'ummar kasar Zimbabwe suka bazama titunan kasar domin yin bore sakamakon kara farashin man fetur a kasar.

A kalla mutane 3 ne suka mutu a sakamakon tashin hankalin yayin da aka balle wasu shaguna da kuma barnata dukiyoyi.

Mnangagwa wanda ya tsara yin bulaguro zuwa Davos a ranar 22 ga watan Janairu zuwa 25 ga watan Janairu. (Ahmad)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China