Fim din wanda aka dauke shi gaba daya a nahiyar Afirka, ya nuna yadda ake yaki da masu farautar namun daji, inda wasu matasan kasar Sin suka nuna himma da kwazo wajen yakar masu farautar namun daji daga kasashe daban-daban a kasar ta Zimbabwe. An dauki fim din a wurare daban-daban na kasar, ciki har da babban lambun shan iska na Zimbabwe, da birnin Harare, da sauran wuraren yawon shakatawa, inda aka nuna kyan yanayin Zimbabwe gami da al'adun gargajiya na kasar.
A nasa bangaren, babban jami'in kula da harkokin siyasa daga ofishin jakadancin Sin dake Zimbabwe, Zhao Baogang ya ce, daukar fim din na daya daga cikin matakan aiwatar da manyan shirye-shirye takwas da aka sanar a wajen taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a takaice, al'amarin da zai taimaka ga karfafa fahimtar juna tsakanin jama'ar Sin da Zimbabwe. Mista Zhao ya kuma ce, kasashen biyu na yin hadin-gwiwa a fannin kare namun daji, kana, Sin za ta ci gaba da marawa Zimbabwe baya wajen yaki da miyagun ayyukan farautar namun dajin.(Murtala Zhang)