in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kusan rabin al'ummar Zimbabwe ne za su yi fama da yunwa a bana saboda fari
2019-03-08 10:24:21 cri

A kalla al'ummar Zimbabwe miliyan 7, ko kusan rabin al'ummar kasar ne za su yi fama da yunwa a bana saboda fari, inda kuma za su bukaci tallafin abinci.

Kamfanin dillancin labarai na kasar New Ziana, ya ruwaito babbar sakatariyar ma'aikatar kwadago da kula da walwalar al'umma Judith Kateera, ta shaida wa wani kwamiti na majalisar dokokin kasar cewa, gwamnatin za ta yi kokarin samar da tallafin abinci ga al'umma, la'akari da yadda yunwa za ta addabi kasar

Judith Kateera ta ce nazarin da majalisar kula da wadatuwar abinci ta yi a watan Junairun bana, shi ne ya bayyana adadin mutanen da matsalar za ta shafa.

Ta ce a bana, mutane kimanin miliyan 7 ne za su yi fama da yunwa, wadanda suka hada da miliyan 4.5 a yankunan karkara da miliyan 3 a yankunan birane. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China