Ministan kula da kananan hukumomi da aikin gwamnati da tsarin samar da gidaje na kasar, July Moyo, ya ce adadin masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da al'amarin ya rutsa da su ka iya kai wa 60 zuwa 70.
Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Juma'a, July Moyo ya ce babu kwakkwarar fatan samu wadanda suka tsira, biyo bayan mamakon ruwa da aka yi a yankin da daren ranar.
Masu aikin ceto sun yi nasarar fitar da ruwa daga cikin ramukan, inda za a fara aikin zakulo gawarwaki a yau Asabar.
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ayyana lamarin a matsayin annobar da ta aukawa kasar.
Ministar kula da harkokin lardin yammacin Mashonaland Mary Mliswa-Chikoka, ta ce lamarin zai zama izina ga hukumomin kula da hakar ma'adinai da masu aikin hakar, kan bukatar rugumar hanyoyin kariya. (Fa'iza Mustapha)