in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da AU sun goyi bayan warware ricikin Libya ta hanyar siyasa
2019-03-14 09:41:15 cri

Mataimakiyar babban sakataren MDD mai kula da harkokin siyasa da samar da zaman lafiya, Rosemary DiCarlo da kwamishinan kungiyar tarayyar Afirka(AU) mai kula da zaman lafiya da tsaro, Ismail Sharqi, sun jaddada goyon bayansu na daidaita ricikin kasar Libya ta hanyar siyasa.

Jami'an biyu sun yi wadannan kalamai ne jiya Laraba, yayin wata ganawa da kwamandan sojojin kasar mai hedkwata a gabashin kasar, janar Khalifa Haftar.

Tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Libya, ta ce tawagogin MDD da AU sun nanata kudirinsu na goyon bayan warware ricikin kasar ta hanyar siyasar ce da nufin ganin an kawo karshen gwamnatin wucin gadi a Libya. A ranar Talata ce, tawagar ta gana da firaministan kasar dake samun goyon bayan MDD Fayez Serraj a Tripoli, babban birnin kasar, inda suka tattauna ci gaba na baya-bayan nan da aka samu a fannonin siyasa da tsaro da ma zabukan da ake fatan shiryawa nan gaba a kasar.

Kasar Libya dai ta fuskanci tashin hankali da rarrabuwar kawunan siyasa tsakanin gwamnatocin yammaci da gabashin kasar, biyon bayan tarzomar shekarar 2011 da ta kai ga hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China