A wani bangare na ziyararsa a Hadaddiya Daular Larabawa, Firaministan gwamnatin Fayez Serraj, ya gana da shugaban kamfanin mai na kasar NOC, Mustafa Sanalla a birnin Abu Dhabi, inda ya amince kamfanin ya dauki matakan tsaron da suka dace a wajen hakar man.
A watan Disamban bara ne kamfanin mai na kasar NOC ya sanar da dakatar da yarjejeniyar aiki a rijiyar Sharara, biyo bayan tilasta musu rufewa da wata kungiyar masu dauke da makamai ta yi.
A baya-bayan nan ne rundunar sojin dake da mazauni a gabashin kasar, ta kwace iko da rijiyar, inda ta yi kira ga kamfanin NOC ya dage batun dakatar da aikin. Sai dai kamfanin, ya bukaci jami'an tsaro su bar wajen kafin a sake budewa. (Fa'iza Mustapha)