in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da 'yan ci rani 160 ne suka nemi komawa gida bisa radin kansu daga Libya
2019-02-23 16:27:18 cri

Hukumar kula da kaura ta duniya IOM, ta sanar da cewa, sama da 'yan ci rani 160 ne suka nemi a mayar da su gida Nijeriya daga Libya.

'Yan ci ranin sun bar birnin Sabha na kudancin Libya ne a wani bangare na shirin hukumar na taimakawa wajen mayar da 'yan ci ranin da suka nemi komawa gida.

IOM ta ce an yi aikin kwashe mutanen ne da taimakon asusun tallafi na Tarayyar Turai.

IOM na gudanar da aikin ne da nufin shirya yadda za a mayar da 'yan ci ranin dake watangarari a Libya zuwa kasashensu na asali.

Matsugunan 'yan ci rani a Libya, na cunkushe ne da dubban 'yan ci ranin da aka ceto daga teku ko kuma wadanda jami'an tsaron kasar suka tsare. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China