in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta jaddada bukatar kawo karshen rikicin siyasar Libya
2019-02-20 09:56:25 cri
Manzon musammam na MDD a Libya, Ghassan Salame, ya jaddada bukatar kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Ghassan Salame ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da Agila Saleh, shugaban majalisar wakilan gwamnatin gabashin kasar.

Wata sanarwa da shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Libya ya fitar, ta ce Ghassan Salame ya jaddada kudurin MDD na aiki tare da al'ummar kasar game da hukumomi ta yadda za su zama na bai daya, da ingiza tattaunawa kan harkokin siyasa da ayyukan majalisun dokoki.

Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma karkashin MDD da kafa gwamnatin hadin kan kasar a 2015, har yanzu Libya na fama da rarrabuwar kawuna saboda siyasa, tsakanin gwamnatocin yammaci da gabashin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China