in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta kwashe bakin haure sama da 4,000 daga Libya
2019-02-04 12:09:17 cri
Hukumar MDD mai lura da 'yan gudun hijira ko UNHCR a takaice, ta kwashe bakin haure sama da 4,000 daga kasar Libya zuwa kasashensu na asali tsakanin shekarar 2018 zuwa watan Janairun 2019n nan.

UNHCR ta ce adadin mutanen da ta sake tsugunarwa, ko ta kwashe daga kasar ya kai mutane 4,080, ta kuma samarwa mutane 34,505 jinya. Kaza lika ta baiwa wasu iyalai su 6, 219 kudaden tallafi, baya ga wasu 1, 311 da aka samarwa tantuna a yankunan kasar inda suka samu mafaka.

Bugu da kari, hukumar ta tabbatar da cewa, ya zuwa yanzu, akwai 'yan gudun hijira da masu neman mafaka da yawansu ya kai 56,643, wadanda ta yi wa rajista a kasar ta Libya.

Kasar Libya ta kasance sansanin yada zango da bakin haure masu yawan gaske ke kaunar shiga, a kan hanyarsu ta tsallakawa yankunan Turai ta Bahar Rum, sakamakon karancin tsaro da kasar ta tsunduma, tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China