in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Libya sun kaddamar da hari ta sama kan mayakan 'yan adawar Chadi a Murzuk
2019-02-04 11:58:26 cri
Dakarun sojin kasar Libya sun kaddamar da hari ta sama kan gungun mayakan 'yan adawar kasar Chadi, a yankin Murzuk mai nisan kilomita 900 daga babban birnin kasar.

Wata sanarwa da ofishin watsa labarai na rundunar sojojin ya fitar, ta ce sojoji masu samun goyon bayan gwamnatin kasar yankin gabashi, sun kaddamar da harin ne da jiragen yaki a jiya Lahadi, sun kuma ci nasarar hallaka mayakan da dama, tare da lalata kayan fadan su.

Sanarwar ta kuma ce karkashin jagorancin kwamanda Janar Khalifa Haftar, sojojin na ci gaba da kaddamar da hare-hare kan 'yan ta'adda, da masu aikata laifuka a kudancin kasar tun daga tsakiyar watan Janairun da ya shude.

Kasar Libya ta kasu gida biyu ta fuskar siyasa, inda gwamnatocin yammaci da na gabashi ke ta hankoron samun karbuwa bisa doka. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China