"Jami'an tsaron birnin Zawiya sun yi nasarar kubutar da ma'aikatan kasar Tunisiya. Ana ci gaba da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa domin tsara hanyoyin da za'a mayar da su ga iyalansu lami lafiya," inji jami'in tsaron birnin Zawiya.
Hukumar tsaron ta tabbatar da cewa ma'aikatan suna cikin koshin lafiya, kuma tuni hukumar ta wallafa hotunansu a shafinta na Facebook.
Haka zalika, ministan harkokin wajen kasar Tunisiya ya tabbatar da sakin ma'aikatan da aka yi garkuwa dasu kuma ya bayyana godiyarsa bisa kokarin da gwamnatin Libyan tayi wajen kubutar da ma'aikatan.
Da yammacin ranar Alhamis ne aka yi garkuwa da ma'aikatan a birnin Zawiya yayin da wasu 'yan binndiga suka yi awon gaba da su zuwa wani wajen da ba'a tantance ba, inji hukumar tsaron Zawiya.
Yan bindigar dai sun bukaci a saki wasu 'yan kasar Libyan da ake tsare da su a Tunisiya a matsayin musaya da ma'aikatan da suka yi garkuwa da su, kamar yadda kafafen yada labaran Tunisiyan suka ambata. (Ahmad Fagam)