in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Za a kara raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga jama'ar Sin da Afirka
2019-03-08 11:47:18 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin kuma mamban majalisar gudanarwar kasar Wang Yi ya bayyana yau cewa, yanzu huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka ta shiga lokaci mafi kyau a tarihi.

Wang Yi ya fadi haka ne a yayin wani taron manema labaru na taro na 2 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC karo na 13. Ya kara da cewa, kasashen Sin da Afirka suna kara samun nasarar hadin kai, yayin da ake ta kara sukarsu da shafa musu kashin kaji. Amma Sin da Afirka suna karawa amincewa da juna sosai, kuma dankon zumunci da ke tsakaninsu ya jure wahalhalu. Haka kuma suna hada kansu a sassa daban daban na nahiyar Afirka. Wasu shugabannin kasashen Afirka da kuma masu idon hangen nesa sun musunta zantukan da ake dangane da basussuka da mulkin mallaka.

Nan gaba za a aiwatar da manyan ayyuka guda 8 da aka gabatar a yayin taron koli na Beijing na tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ta FOCAC, da kuma hadin kan bangarorin biyu bisa shawarar "Ziri daya da Hanya daya", a kokarin yin amfani da wadannan damammaki 2 wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga jama'ar Sin da Afirka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China