Wang Yi: tunanin diplomasiyya na Xi Jinping tushe ne na manufofin diplomasiyya na kasar Sin a sabon zamani
Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yayin taro na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a yau Juma'a cewa, an tabbatar da tunanin diplomasiyya na shugaba Xi Jinping a matsayin abin jagora a gun taron ayyukan diplomasiyya na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na shekarar 2018. Wang Yi ya ce wannan muhimmin sakamako ne wajen kyautata manufofin diplomasiyya na kasar Sin, kana ya zama tushen manufofin harkokin waje na Sin a sabon zamani, tare da nuna hanyoyi da suka dace na daidaita matsalolin duniya a halin yanzu. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku