Jakadan kasar Ghana dake kasar Sin Edward Boateng ya bayyana a kwanan nan a birnin Beijing cewa, ya kamata kasashen Afirka ciki har da kasar Ghana su yi amfani da damar da kasar Sin ke samarwa ta bude kofa ga waje, da kuma inganta hadin gwiwa tare da Sin a fannin raya aiki karkarshin laimar shawarar "Ziri daya da Hanya daya".
Game da rahoton aikin gwamnatin Sin da firaminitan kasar Li Keqiang ya gabatar a taron shekara shekara na majalisar NPC na bana kuwa, Jakada Boateng wanda ya halarci taron bisa gayyatar da aka yi masa ya yi matukar jinjina, inda ya ce, rahoton ya shafi fannoni daban daban, wanda ya nuna muhimmancin da gwamnatin Sin ke dorawa jama'arta. Yayin da kasar ke neman samun bunkasuwa, da kyautata zaman rayuwar jama'arta, musamman inda kasar ta Sin ta samu babbar nasara a fannin yaki da talauci bisa halin da ake ciki. Lallai ya kamata kasashe masu tasowa ciki har da kasashen Afirka su yi koyi daga wajenta.(Kande Gao)