Ministan harkokin kudi na kasar Sin Liu Kun ya bayyana yau Alhamis a birnin Beijing, cewar yadda aka yi hasashen gibin GDP na kasar Sin a wannan shekarar da muke ciki ya yi daidai.
A cikin rahoton aikin da gwamnatin kasar Sin ta gabatar wa taron shekara-shekara na majalisar NPC don tantancewa, an nuna cewa, an yi hasashen cewa, jimillar gibin GDP na kasar Sin na shekarar 2019 zai kai kashi 2.8 bisa ciki, wadda ta karu da kashi 0.2 cikin dari bisa na kasafin kudin Sin na bara. Game da batun, Mr. Liu ya furta a yayin taron manema labarai da aka yi a yau, cewar kara jimillar gibin GDPn na bana da Sin ta yi zai kara daidaitawa da ma bunkasar tattalin arziki, baya ga daidaita batun rage harajin da za a biya, da rage wa masana'antu karin nauyi, da ma kara inganta harkokin kasuwanci.
Liu Kun ya kara da cewa, jimillar gibin GDPn da kasar Sin ta tsara a bana ta karu da Yuan biliyan 380 bisa ta bara, amma ba ta kai kashi 3 cikin dari da duniya ta amince da shi ba, don haka gibin na kasar Sin ba shi da yawa idan an kwatanta da na manyan kasashe da yankuna masu karfin tattalin arziki a duniya.(Kande Gao)