in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping da firaminista Li Keqiang sun halarci zaman tattaunawa da wakilai daga wasu larduna
2019-03-08 10:17:36 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang sun halarci zaman tattaunawa da wakilai daga wasu lardunan kasar masu halartar taro na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a jiya Alhamis.

A yayin zaman tattaunawa da wakilai daga lardin Gansu, Xi Jinping yana fatan jami'ai da jama'ar lardin Gansu su bi hanya mai dacewa wajen yaki da talauci, da kara taimakawa garuruwa masu talauci, da matalauta dake kauyuka.

A yayin zaman tattaunawa da wakilai daga lardin Qinghai kuwa, Li Keqiang ya bayyana cewa, ya kamata a bi sabon tunanin samun ci gaba, da yin hadin gwiwa wajen sa kaimi ga aikin kiyaye muhalli, da tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata da kuma raya shi ba tare da gurbata yanayi ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China