in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan Sinawa masu fama da fatara ya ragu da miliyan 80 a cikin shekaru shida da suka wuce
2019-03-07 14:42:30 cri
Shugaban ofishin ba da jagoranci kan ayyukan yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin Liu Yongfu, ya bayyana a yau Alhamis a birnin Beijing cewa, a cikin shekaru shida da suka gabata bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yaki da talauci bisa yanayin da ake ciki, yawan matalauta ya ragu daga miliyan 98.99 na shekarar 2012 zuwa miliyan 16.6 a shekarar 2018, lamarin da ya sa yawan matalautan ya ragu da miliyan 80 gaba daya. A cikin larduna 8 daga cikin 9 a gabashin kasar Sin, an riga an kawar da talauci baki daya. A shekarar da muke ciki kuma, kasar Sin za ta kokarta domin ganin samun raguwar yawan masu fama da fatara da ya zarce miliyan 10.

A gun taron manema labarai da aka kira yau yayin taron shekara shekara na majalisar NPC, Mr. Liu ya ce, manufar gudanar da aikin yaki da talauci da kasar Sin ke yi ita ce warware matsalar fatara da ta addabi Sinawa cikin shekaru fiye da dubu daya. Samun nasarar fama da kangin talauci ba ya nufin babu kasancewar talauci a kasar Sin, akwai shi daidai gwargwado. Ban da wannan kuma ya furta cewa, kawo yanzu kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, wannan wani halin musamman ne na bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Sin, don haka aikin yaki da talauci ya zama wani aiki ne a gaban kasar Sin cikin dogon lokaci.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China