in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin a Afirka ta Kudu ya musunta wasu rahotanni game da jihar Xinjiang ta kasar Sin
2019-03-08 11:09:22 cri

Lin Songtian, jakadan kasar Sin da ke kasar Afirka ta Kudu ya gana da wasu kafofin yada labari na kasar a jiya, domin yin karin bayani kan yadda jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ke sabunta hanyoyin samun nasarar yaki da ta'addanci da kuma nasarorin da kasar Sin ta samu wajen kare hakkin dan Adam.

A kwanakin baya ne, wasu kafofin yada labaru na Afirka ta Kudu suka ruwaito labarun takwarorinsu na kasashen yammacin duniya, wadanda suka yi zargin kan 'yancin bin addini a jihar Xinjiang da kuma batun kare hakkin dan Adam a kasar Sin.

Dagane da hakan, jakada Lin Songtian ya nuna cewa, zargin da kasashen yammacin duniya suka yi wa kasar Sin dangane da tauye 'yancin bin addini, ba shi da tushe balle makama, yana mai cewa karya ce kawai. Ya ce al'ummar Xinjiang suna cikin babban iyalin al'ummar Sin, kuma suna bin addini cikin 'yanci. Ya ce a jihar Xinjiang kawai, akwai masallatai dubu 24 da dari 4. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China