in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ta karyata zargin da Turkiyya ta yi kan batun Xinjiang
2019-02-11 20:30:49 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madam Hua Chunying ta karyata zargi da sukar da takwaranta na kasar Turkiyya ya yiwa kasar Sin kan batun jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta.

A yayin taron manema labarai da aka yi a yau Litinin, Madam Hua ta ce, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ya ce wai shahararren mawaki dan kabilar Uygur Abdurrehim Heyit ya rasa ransa a shekararsa ta biyu a gidan yari, amma gaskiyar maganar ita ce, mawakin yana nan raye lafiyarsa kalau.

Madam Hua ta kara da cewa, ko a jiya ma ta kalli wani hoton bidiyonsa ta kafar Intanet. Ta ce, Turkiyya ta yi wannan zuki ta malle har ta jirgita gaskiya gami da zargin kasar Sin, kuma wannan babban kuskure ne da gwamnatin kasar Sin ta ki amincewa da shi sam.

Madam Hua ta sake jaddada cewa, a yayin da take koyon fasahohin yaki da ta'addanci daga sauran kasashen duniya, jihar Xinjiang tana kuma nuna himma da kwazo wajen yakar ayyukan ta'addanci da kawar da masu tsattsauran ra'ayin addini, kuma ta samu nasarori masu tarin yawa. A halin yanzu al'ummar jihar Xinjiang na kara jin dadin zaman rayuwarsu. Hua ta kara da cewa, 'yan kabilu daban-daban a jihar ta Xinjiang suna da 'yancin bin addininsu da 'yancin yin amfani da yare da kalamai na kabilunsu bisa doka.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China