in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane fiye da miliyan 150 sun ziyarci jihar Xinjiang ta kasar Sin a shekarar 2018
2019-01-16 10:55:47 cri
Wani labarin da aka samu daga tarukan majalissun jihar Xinjiang ta Uygur ta kasar Sin ya nuna cewa, a cikin shekarar 2018, yawan mutanen da suka yi yawon shakatawa a jihar ya zarce miliyan 150, adadin da ya karu da kashi 40% idan an kwatanta da na shekarar 2017.

An ce ci gaban sana'ar yawon shakatawa a jihar Xinjiang a bara, ta kara fadada, hakan kuma bai tsaya a wasu lokuta mafi samun masu yawon bude ido irinsu lokacin zafi, da kaka kadai ba, domin a wasu yankunan jihar irinsu Urumchi, da Altai, ko a lokacin sanyi ma, ana kokarin raya harkar yawon shakatawa. Ga misali, a yankin Altai, inda ake samun dimbin kankara a lokacin sanyi, ana ta kokarin hadin kai da kamfanonin yawon shakatawa na wurare daban daban na kasar Sin, don yayata ra'ayin wasan kankara. Yanzu wannan dabara ta zamanto wata sana'ar da ke tura tattalin arzikin wurin gaba, kuma ta sa kudin da ake samu a fannin yawon shakatawa ya karu da kashi 105% a shekarar 2018, bisa na shekarar 2017.

Shirin da aka gabatar cikin rahoton aikin gwamnatin jihar Xinjiang ya tanaji cewa, a nan gaba za a kara kokarin raya harkar yawon shakatawa, don mai da ita wani ginshikin tattalin arziki, haka kuma za a mai da Xinjiang ta zama wani wurin da masu yawon bude ido na kasashe daban daban ke sha'awar zuwa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China