Tawagar ta ce, nasarar da gwamnatin kasar Sin ta samu wajen kula da harkokin yankin, abin a yaba ne.
'Yan jaridun da suka fito daga kasashen dake hanyar siliki, sun kawo ziyara kasar Sin ne daga ranar 9 zuwa 16 ga watan Janairu. 'Yan jaridun dai sun fito ne daga kasashen Masar da Turkiyya da Afghanistan da Bangladesh da kuma Sri Lanka, inda suka ziyarci mazauna yankin na Xinjiang da kuma cibiyar koyar da sana'o'i. (Ibrahim)