Game da kalaman da wasu kasashe suka yi kan jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur ta kasar Sin, Yu ya nuna cewa, sun dauki irin wannan ra'ayin ne sakamakon son zuciya da yanke shawara bisa kuskure kan kasar Sin, ba su dace ba da ainihin yanayin da ake ciki. Yu ya kara da cewa, "Gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakan yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi ne a jihar Xinjiang da nufin taimakawa wasu mutane kadan da aka yi musu tasiri sakamakon tsattsauran ra'ayi, don su kawar da ra'ayin ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, da sake komawa zamantakewar al'umma. An gudanar da matakan ne bisa doka, wadanda suka kyautata yanayin tsaro na jihar Xinjiang har ma na kasar ta Sin baki daya, ta yadda suka ba da tabbaci ga hakkin bil Adam na jama'ar kabilu daban daban na kasar, wadanda ke samun goyon baya daga wajen jama'a."
Baya ga haka, Yu ya bayyana cewa, akwai kabilu 56 a nan kasar Sin, 'yan kabilu daban daban na zama tare da juna kamar yadda 'yan uwa suke yi, dukkansu mambobi ne na babban iyalin kasar Sin. Kasar Sin na maraba da mutane masu neman jin ra'ayi na bisa hakikanin hali da adalci su kai ziyara a jihar ta Xinjiang. (Bilkisu)