Bisa goron gayyatar da ofishin kula da harkokin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin da ofishin jakadancin kasar Sin da ke Masar suka ba ta, daga ranar 25 zuwa ranar 31 ga watan Janairun da ya gabata, wata tawagar 'yan jaridu da ta hada jaridar al-Ahram, da jarida al-Gomhuriya da gidan talabijin na Nilu da sauransu, sun kai ziyara jihar Xinjiang ta kasar Sin.
Bayan da 'yan jaridar suka ganewa idonsu yadda mazauna jihar suke rayuwa cikin jituwa da ma yin hira da dalibai dake cibiyar koyar da ilmin sana'o'i, sun bayyana cewa, matakin da kasar Sin ta dauka na kawar da tsattsauran ra'ayi daga tushe mataki ne mai amfani wajen yakar ta'addanci da kawar da tsattauran ra'ayi a sabon yanayin da ake ciki.