Da yake jawabi a gaban wakilan wani taro na " Road to Davos" wanda ya gudana a ranar Juma'a, a Harare, Ncube ya ce, amfani da dalar Amurka ko kuma kudin rand na kasar Afrika ta kudu ba zai iya magance matsalolin tattalin arzikin kasar ba.
Da aka tambaye shi ko zuwa yaushe ne sabbin kudaden na cikin gida zasu fara aiki, Ncube ya ce, komai zai kammala ne kasa da watanni 12.
Zimbabwe ta kaddamar da shirin amfani da nau'o'in kudade a kasar a shekarar 2009, bayan da darajar kudin kasar ta fadi kasa warwas a sakamakon mummunan tashin farashin kayayyaki a kasar.