Mnangagwa dai ya doke abokin hamayyarsa na jam'iyyar kawance ta MDC Nelson Chamisa da karamin rinjaye, inda jam'iyyar ZANU-PF ta lashe kaso 2 bisa 3 na kujerun majalisar dokokin kasar, ta kuma lashe galibin kujerun majalisun kananan hukumomin kasar, yayin da jam'iyyar MDC ta yi galaba a yankunan biranen kasar.
Sai dai kuma Chamisa da jam'iyyarsa ta MDC sun yi fatali da nasarar da Mnangagwan ya samu, inda a karshen watan Nuwamba suka shirya bore a Harare, babban birnin kasar don nuna rashin amince da sakamakon zaben da ma yanayin tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
'Yan adawar dai na bukatar Mnangagwa da su hau teburin tattaunawa, yana mai cewa jam'iyya mai mulki ita kadai ba za ta iya magance matsalar tattalin arzikin kasar ita kadai ba. (Ibrahim)