in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya su tallafawa tattalin arzikin Sudan ta Kudu
2018-11-17 15:52:21 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya yi kira ga kasashen duniya su samar da agajin jin kai tare da taimakawa tattalin arzikin Sudan ta Kudu.

Ma Zhaoxu ya shaidawa taron kwamitin sulhu kan Sudan ta Kudu cewa, yayin da kasar ta tsinci kanta cikin rikicin da ya shafe lokaci mai tsawo, ci gaban tattalin arziki da na zaman takewa sun samu koma baya, sannan an gaza samar da ababen more rayuwa.

Ya bukaci kasashen duniya su kara tallafawa tattalin arzikin kasar, musamman a fannonin aikin gona da makamashi da samar da ababen more rayuwa da ilimi da kiwon lafiya.

Ya ce ya kamata a girmama matsayin kasar na kula da harkokin cikin gidanta, tare da karfafawa gwamnatin kasar giwar taka rawar da ya kamata. Sannan kasa da kasa su bada tallafin da ya dace da bukatun kasar da na al'ummarta tare kuma da kaucewa danniya.

Har ila yau, jakadan na kasar Sin, ya kuma jadadda muhimmancin rawar da mata za su taka wajen sake gina kasar, ya na mai cewa kasar Sin na mara baya ga matan kasar, da su taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da yarjejeniyar warware rikicin kasar da aka farfado da ita, tare kuma da mara baya ga gwamnati wajen kare hakkokin mata da na yara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China