in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi tir da cin zarafin mata da aka yi a Sudan ta Kudu
2018-12-10 11:21:26 cri
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da ayyukan da suka shafi cin zarafin mata ta hanyar lalata da aka yi kwanakin baya a yankin Bentiu dake arewacin kasar Sudan ta Kudu.

Cikin wata sanarwar da aka fitar a daren ranar Asabar din da ta gabata, kwamitin tsaron ya bayyana matukar damuwa kan halin da matan da abun ya shafa suke ciki, wadanda rahotanni suka ruwaito cewa, akwai mata da 'yan mata sama da 150 wadanda wasu 'yan bindiga sanye da kayan soja da na fararen-hula suka kaiwa hari a yankunan dake hannun gwamnati a gundumar Rubkona.

Kwamitin tsaron ya kuma yi kira ga gwamnatin Sudan ta Kudu da ta yi tir da wadannan hare-hare, da tabbatar da gudanar da cikakken bincike da yankewa wadanda suka aikata laifin hukunci, ta yadda zai zama izina ga masu aikata laifin cin zarafin mata da 'yan mata ta hanyar lalata.

Har wa yau, kasashe membobin kwamitin tsaron MDD sun jaddada cewa, kamata ya yi a yanke hukunci mai tsanani kan mutanen da suka aikata laifin keta dokar jin-kai ta duniya, da wadanda suka aikata laifin keta hakkokin jama'a. Kana, ya zama dole gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta dauki babban nauyin kare daukacin jama'arta daga laifuffukan da aka aikata musu, ciki har da kisan kiyashi, da laifukan yaki, da kisan kare-dangi da dai sauran laifuffukan da suka shafi keta hakkokin jama'a.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China